Dandalin Halal na Shaidun Jehobah

Gida Beliefs Future Medical Topics Contact Us Publications Languages

Shaidun Jehovah—Su Wanene ne Su? Menene Suka Gaskata?

Talifa na bayaTalifi na gaba

Menene Suka Gaskata?

SHAIDUN JEHOVAH sun gaskata da Maɗaukaki Allah, Jehovah, Mahaliccin sama da ƙasa. Abubuwa masu wuya da suke wanzuwa, da ke na al’ajabi a duniya da suka kewaye mu sun nuna cewa Mahalicci mai basira da kuma iko ne ya yi su duka. Yadda ayyukan maza da mata ke nuna halayensu, haka ma na Jehovah Allah suke nuna nasa. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa ‘tun halittar duniya al’amura nasa da ba su ganuwa, ta wurin abubuwa da an halitta ana ganinsu.’ Haka ma, ba tare da murya ba ko kuma kalmomi ‘sammai suna bayana ɗaukakar Allah.’—Romawa 1:20; Zabura 19:1-4.

Jehovah ya halicce . . . DUNIYA . . . ya sa mutane su kula da ita . . . su zauna har abada a cikinta

Mutane ba sa mulmula tukwanen ƙasa ko kuma su yi telibijin da kwamfita ba tare da wani dalili ba. Halittar duniya ta tsiro da ta dabbobi sun fi ban mamaki. Ba za mu iya gane yadda aka yi jikin mutum da biliyoyin ƙwayoyin gina jiki ba—ƙwaƙwalwa ma da muke yin tunani da ita aba ce ta ban al’ajabi! Idan mutane suna da dalilin da ya sa suka ƙera abubuwa da ba su da muhimmanci, hakika Jehovah Allah yana da dalilin halitta da ya yi, masu ban mamaki! Misalai 16:4 ya ce “Ubangiji ya halicci kowane abu domin nufin kansa.”


Jehovah yana da dalilin da ya sa ya yi duniya, yadda ya gaya wa mutane biyu na fari: “Ku yalwata da ’ya’ya, ku riɓu, ku mamaye duniya . . . ku yi mulkin kifaye na teku, da tsuntsaye na sarari, da kowane abu mai-rai wanda ke rarrafe a ƙasa.” (Farawa 1:28) Domin sun yi rashin biyayya, wannan mata da miji sun kasa cika duniya da iyalai masu adalci da za su kula da duniya da tsire-tsire da dabbobinta da kyau. Amma kasawarsu ba ta sa nufin Jehovah ya susuce ba. Shekaru dubbai daga baya, aka rubuta: “Allah; mai-sifanta duniya . . . , ya halicce ta ba wofi ba.” Ya “kamanta ta domin wurin zama.” Ba za ta halaka ba, amma “duniya kuwa ta dawwama.” (Ishaya 45:18; Mai-Wa’azi 1:4) Za a gano nufin Jehovah game da duniya: “Ƙudurina za ya tabbata, zan kuma cika dukan nufina.”—Ishaya 46:10.

Saboda haka, Shaidun Jehovah suka gaskata cewa duniya za ta kasance har abada, kuma dukan mutane rayayyu da matattu, da za su jitu da nufin Jehovah game da duniya mai kyau za su zauna a cikinta har abada. Dukan mutane sun gaji ajizanci daga Adamu da Hauwa’u, saboda haka dukan mutane masu zunubi ne. (Romawa 5:12) Littafi Mai Tsarki ya gaya mana: “Hakkin zunubi mutuwa ne.” “Masu-rai sun san za su mutu: amma matattu ba su san kome ba.” “Mai-rai da ya yi zunubi, shi za ya mutu.” (Romawa 6:23; Mai-Wa’azi 9:5; Ezekiel 18:4, 20) Ta yaya za su rayu kuma su sami albarka ta duniya? Sai ta hadayar fansa na Kristi Yesu, gama ya ce: “Ni ne tashin matattu, ni ne rai: wanda ya bada gaskiya gareni, ko ya mutu, za shi rayu.” “Dukan waɗanda suna cikin kabarbaru za su ji muryatasa, su fito kuma.”—Yohanna 5:28, 29; 11:25; Matta 20:28.

Yaya wannan zai faru? An yi bayani cikin “bishara ta mulkin,” da Yesu ya soma yi lokacin da yake duniya. (Matta 4:17-23) A yau Shaidun Jehovah suna yin wa’azin bishara a hanya ta musamman.

ABIN DA SHAIDUN JEHOVAH SUKA GASKATA

Imani Dalilai na Nassi
Littafi Mai Tsarki Kalmar Allah ne kuma gaskiya ne 2 Tim. 3:16, 17; 2 Bit. 1:20, 21; Yoh. 17:17
Littafi Mai Tsarki ya fi al’ada tabbaci Mat. 15:3; Kol. 2:8
Sunan Allah Jehovah ne Zab. 83:18; Isha. 26:4; 42:8, AS; Fit. 6:3
Kristi Ɗan Allah ne, kuma bai kai Allah ba Mat. 3:17; Yoh. 8:42; 14:28; 20:17; 1 Kor. 11:3; 15:28
Kristi ne na farko a cikin abubuwa da Allah ya halitta Kol. 1:15; R. Yoh. 3:14
Kristi ya mutu a kan gungume ne, ba a kan gicciya ba Gal. 3:13; Ay. Man. 5:30
Kristi ya ba da ransa na mutum fansa domin mutane masu biyayya Mat. 20:28; 1 Tim. 2:5, 6; 1 Bit. 2:24
Hadayar Kristi kaɗai ta isa Rom. 6:10; Ibran. 9:25-28
An tashi Kristi daga matattu ya zama ruhu mara mutuwa 1 Bit. 3:18; Rom. 6:9; R. Yoh. 1:17, 18
Bayyanuwar Kristi a ruhu ne Yoh. 14:19; Mat. 24:3; 2 Kor. 5:16; Zab. 110:1, 2
Yanzu muna ‘lokaci na ƙarshe’ Mat. 24:3-14; 2 Tim. 3:1-5; Luka 17:26-30
Mulki a ƙarƙashin Kristi zai yi sarautar duniya cikin adalci da salama Isha. 9:6, 7; 11:1-5; Dan. 7:13, 14; Mat. 6:10
Mulkin zai kawo yanayin rayuwa mai kyau a duniya Zab. 72:1-4; R. Yoh. 7:9, 10, 13-17; 21:3, 4
Duniya ba za ta taɓa halaka ba ko kuma jama’a su ƙare Mai-Wa. 1:4; Isha. 45:18; Zab. 78:69
Allah zai kawar da tsarin abubuwa na yanzu a yaƙin Har–Magedon R. Yoh. 16:14, 16; Zeph. 3:8; Dan. 2:44; Isha. 34:2; 55:10, 11
Za a halaka miyagu har abada Mat. 25:41-46; 2 Tass. 1:6-9
Mutane da Allah ya amince da su za su sami rai madawwami Yoh. 3:16; 10:27, 28; 17:3; Mar. 10:29, 30
Hanya ɗaya ce kaɗai zuwa rai Mat. 7:13, 14; Afis. 4:4, 5
Mutuwa da ’yan Adam suke yi domin zunubin Adamu ne Rom. 5:12; 6:23
Kurwan ’yan Adam ba ta wanzuwa bayan an mutu Eze. 18:4; Mai-Wa 9:10; Zab. 6:5; 146:4; Yoh. 11:11-14
Jahannama kabari ne na mutane Ayu. 14:13 Dy; R. Yoh. 20:13, 14, AV (hasiya)
Tashin matattu ne begen matattu 1 Kor. 15:20-22; Yoh. 5:28, 29; 11:25, 26
Mutuwar da Adamu ya jawo za ta ƙare 1 Kor. 15:26, 54; R. Yoh. 21:4; Isha. 25:8
Ƙaramin garke 144,000 ne kawai za su je sama su kuma yi sarauta tare da Kristi Luka 12:32; R. Yoh. 14:1, 3; 1 Kor. 15:40-53; R. Yoh. 5:9, 10
An sake haifan 144,000 sun zama ’ya’yan Allah na ruhu 1 Bit. 1:23; Yoh. 3:3; R. Yoh. 7:3, 4
An yi sabon alkawari da Isra’ila ta ruhaniya Irm. 31:31; Ibran. 8:10-13
An gina ikilisiya ta Kristi a kansa ne Afis. 2:20; Ish. 28:16; Mat. 21:42
Ga Jehovah ne kaɗai za a yi addu’a ta wurin Kristi Yoh. 14:6, 13, 14; 1 Tim. 2:5
Bai kamata a yi amfani da sifoffi ba wajen bauta Fit. 20:4, 5; Lev. 26:1; 1 Kor. 10:14; Zab. 115:4-8
Tilas ne a ƙi sihiri K. Sha 18:10-12; Gal. 5:19-21; Lev. 19:31
Shaiɗan ne mai sarauta mara ganuwa a duniya 1 Yoh. 5:19; 2 Kor. 4:4; Yoh. 12:31
Bai kamata Kirista ya yi hulɗa da ƙungiyoyin addinai ba 2 Kor. 6:14-17; 11:13-15; Gal. 5:9; K. Sha 7:1-5
Ya kamata Kirista ya kasance a ware daga duniya Yaƙ. 4:4; 1 Yoh. 2:15; Yoh. 15:19; 17:16
Suna yin biyayya ga dokokin mutane da ba su saɓa ba da dokokin Allah Mat. 22:20, 21; 1 Bit. 2:12; 4:15
Karɓa ƙarin jini ta baki ko ta jijiya karya dokokin Allah ne Far. 9:3, 4; Lev. 17:14; Ay. Man. 15:28, 29
Dole ne a yi biyayya ga dokokin Littafi Mai Tsarki a kan ɗabi’u 1 Kor. 6:9, 10; Ibran. 13:4; 1 Tim. 3:2; Mis. 5:1-23
Isra’ila ce kaɗai aka ba dokar bin Assabaci kuma ta ƙare da Dokar Musa K. Sha 5:15; Fit. 31:13; Rom. 10:4; Gal. 4:9, 10; Kol. 2:16, 17
Ajin limamai da laƙabi na musamman ba daidai ba ne Mat. 23:8-12; 20:25-27; Ayu. 32:21, 22
Mutum bai bayyana kawai ba amma an halicce shi ne Isha. 45:12; Far. 1:27; Mat. 19:4
Dole ne a bi misalin da Kristi ya kafa a bauta wa Allah 1 Bit. 2:21; Ibran. 10:7; Yoh. 4:34; 6:38
Yin baftisma ta wurin nutsarwa gaba ɗaya cikin ruwa yana nuna keɓe kai Mar. 1:9, 10; Yoh. 3:23; Ay. Man. 19:4, 5
Kiristoci da farin ciki suna ba da shaida ta gaskiyar Nassi ga jama’a Rom. 10:10; Ibran. 13:15; Isha. 43:10-12
 

An Wallafa a Shekara ta 2000

GidaSama Talifa na bayaTalifi na gaba

Copyright © 2006 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania. All rights reserved.