Dandalin Shaidun Jehobah

Gida Beliefs Future Medical Topics Ka Tuntuɓe Mu Publications Languages

Shaidun Jehovah—Su Wanene ne Su? Menene Suka Gaskata?

Talifa na baya

Muna Gayyatarka

Mun ji daɗin yi maka magana ta wurin shafuffukan wannan mujallar. Muna fata ka ji daɗin ƙara ilimi game da Shaidun Jehovah. Don Allah, muna gayyatarka ka ziyarce mu a Majami’ar Mulkinmu. Ka ga yadda ake tafiyar da taronmu. Ka kuma ga yadda muke ƙoƙari mu yi wa wasu bishara ta aljanna a duniya a ƙarƙashin Mulkin Kristi.

Allah ya yi alkawari. “Bisa ga alkawarinsa, muna sauraron sababbin sammai da sabuwar duniya, inda adalci ya ke zaune.” (2 Bitrus 3:13) Ƙarnuka da yawa sun wuce. Lokacin jira yana matso ƙarshensa. Yanayin duniya ya nuna wannan.

“Da kuna ganin ranar nan tana gusowa,” manzo Bulus ya ce, “mu lura da juna domin mu tsokani juna zuwa ga ƙauna da nagargarun ayyuka; kada mu fasa tattaruwanmu.” (Ibraniyawa 10:24, 25) Muna gayyatarka ka yi biyayya ga gargaɗin Bulus ta wurin haɗuwa da mu.

Za ka yarda a ziyarce ka?

 

An Wallafa a 2000

GidaSama Talifa na baya