Dandalin Halal na Shaidun Jehobah

Gida Beliefs Future Medical Topics Contact Us Publications Languages
Menene Allah Yake Bukata a Garemu? Darasi na 3Talifa na bayaTalifi na gaba

Wanene Yesu Kristi?

Me ya sa ake kiran Yesu Ɗan “fari” na Allah? (1)
Me ya sa ake kiransa “Kalma”? (1)
Me ya sa Yesu ya zo duniya cikin siffar mutum? (2-4)
Me ya sa ya yi mu’ujizoji? (5)
Menene Yesu zai yi a nan gaba kaɗan? (6)

1. Yesu ruhu ne a sama kafin ya zo duniya. Shi ne halittar Allah ta fari, kuma don haka ake kiransa Ɗan “fari” na Allah. (Kolossiyawa 1:15; Ru’ya ta Yohanna 3:14) Yesu ne kawai Ɗa da Allah ya halitta da kansa. Jehovah ya yi amfani da Yesu ‘gwanin aikinsa’ wajen halittan dukan sauran abubuwa da ke sama da kuma duniya kafin ya zama mutum. (Misalai 8:22-31; Kolossiyawa 1:16, 17) Allah ya yi amfani da shi ya zama babban Wakilinsa wurin magana. Shi ya sa aka kira Yesu “Kalma.”—Yohanna 1:1-3; Ru’ya ta Yohanna 19:13.

2. Allah ya aiko Ɗansa duniya ta wurin ƙaurar da ransa zuwa mahaifar Maryamu. Saboda haka, Yesu ba shi da uba ɗan Adam. Shi ya sa bai gāji zunubi ba ko ajizanci. Allah ya aiko Yesu duniya domin dalilai uku: Na (1) don ya koya mana gaskiya game da Allah (Yohanna 18:37), na (2) don ya riƙe gaskiya sosai, ya bar mana tafarki da za mu bi (1 Bitrus 2:21), na (3) kuma don ya sadaukar da ransa ya ’yantar da mu daga zunubi da kuma mutuwa. Me ya sa ake bukatar wannan?—Matta 20:28.

3. Lokacin da Adamu, mutum na fari, ya taka dokar Allah, ya aikata abin da Littafi Mai-Tsarki ya kira “zunubi.” Don haka Allah ya yanke masa hukuncin kisa. (Farawa 3:17-19) Bai kai ga mizanan Allah kuma ba, saboda haka ya zama ajizi. Da sannu sannu ya tsufa kuma ya mutu. Adamu ya bar zunubi akan dukan yaransa. Shi ya sa mukan tsufa, mukan yi ciwo, kuma mu mutu. Ta yaya za a ceci ’yan Adam?—Romawa 3:23; 5:12.

4. Yesu kamiltaccen mutum ne kamar Adamu. Amma dai, Yesu ya yi biyayya ga Allah sosai, har ma a lokacin gwaji mafi wuya ba kamar Adamu ba. Saboda haka zai iya sadaukar da kamiltaccen ransa na mutum don biyan zunubin Adamu. Wannan shi ne abin da Littafi Mai-Tsarki yake nufi da “fansa.” Saboda haka, za a iya sake ’ya’yan Adamu daga hukuncin kisa. Dukan waɗanda suka ba da gaskiya ga Yesu za a gafarta masu zunubansu kuma za su sami rai na har abada.—1 Timothawus 2:5, 6; Yohanna 3:16; Romawa 5:18, 19.



Hidimar Yesu ta ƙunshi koyarwa, yin mu’ujizoji, har ma da ba da ransa dominmu

5. Lokacin da Yesu yake duniya ya warkar da marasa-lafiya, ya ciyar da mayunwata, ya tsayar da guguwa. Har ma ya tada matattu. Me ya sa ya yi mu’ujizoji? Na (1) ya ji tausayin mutane da suke shan wahala, kuma ya so ya taimake su. Na (2) mu’ujizojinsa sun tabbatar da cewa shi Ɗan Allah ne. Na (3) sun nuna abin da zai yi wa mutane masu biyyaya yayin da ya fara Sarauta bisa duniya.—Matta 14:14; Markus 2:10-12; Yohanna 5:28, 29.

6. Yesu ya mutu amma Allah ya tashe shi ya zama halittar ruhu, kuma ya koma sama. (1 Bitrus 3:18) Tun wannan lokacin, Allah ya naɗa shi Sarki. Ba da daɗewa ba Yesu zai kawar da dukan mugunta da wahala daga duniyar nan.—Zabura 37:9-11; Misalai 2:21, 22.

 

An Wallafa a Shekara ta 1996

GidaSamaTalifa na bayaTalifi na gaba

Copyright © 2006 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania. All rights reserved.