| Menene Allah Yake Bukata a Garemu? | Darasi na 4 |
Wanene Iblis? |
|
| Shaiɗan Iblis—daga ina ya fito? (1, 2) | |
| Ta yaya Shaiɗan yake yaudarar mutane? (3-7) | |
| Me ya sa ya kamata ka yi hamayya da Iblis? (7) | |
1. Kalmar nan “iblis” tana nufin wanda yake muguwar ƙarya game da wani. “Shaiɗan” yana nufin abokin gāba ko kuma ɗan hamayya. Waɗannan sune kalmomi da ake kiran babban abokin gāban Allah da su. Da farko, kamiltaccen mala’ika ne da ke tare da Allah a sama. Amma, daga baya ya ɗauki kansa fiye da yadda ya kamata kuma ya so a bauta masa, bauta kuma ta Allah ce.—Matta 4:8-10.
2. Wannan mala’ika, Shaiɗan, ya yi amfani da maciji wajen magana da Hawa’u. Ta wurin ƙarya da ya yi mata, ya sa ta yi rashin biyyaya wa Allah. Da haka Shaiɗan ya yi farmaki ga abin da aka kira “ikon mallaka” na Allah, ko kuwa matsayinsa na Maɗaukaki. Shaiɗan ya tuhumi Allah da cewa ba ya sarauta a hanyar da ta cancanta don bayinsa su amfana. Ƙari ga haka Shaiɗan ya tuhumi amincin ’yan Adam ga Allah. Da ya yi wannan, Shaiɗan ya mai da kansa abokin gāban Allah. Abin da ya sa aka kira shi Shaiɗan Iblis ke nan.—Farawa 3:1-5; Ayuba 1:8-11; Ru’ya ta Yohanna 12:9. 3. Shaiɗan ya yi ƙoƙarin ya ruɗe mutane su bauta masa. (2 Korinthiyawa 11:3, 14) Hanya ɗaya da yake yaudarar mutane ita ce ta addinin ƙarya. Addinin da yake koyar da ƙarya game da Allah, babu shakka yana cika nufin Shaiɗan ne. (Yohanna 8:44) Mutane da suke yin addinan ƙarya sai su yarda da gaske cewa suna bauta wa Allah na gaskiya. Amma hakika, Shaiɗan suke yi wa bauta. Shi ne ‘allah na wannan duniya.’—2 Korinthiyawa 4:4.
4. Sihiri wata hanya ce da Shaiɗan yake jawo mutane ƙarƙashinsa. Za su iya kiran iskoki don su tsare su, don su naƙasa wasu, don su yi duba, ko kuwa don su yi mu’ujizoji. Shaiɗan ne mugun da ke goyon bayan dukan waɗannan ayyuka. Don mu faranta wa Allah rai, dole ne mu ƙi sihiri.—Kubawar Shari’a 18:10-12; Ayukan Manzanni 19:18, 19. 5. Shaiɗan yana kuma yaudarar mutane ta wurin yawan alfahari na ƙabila da kuma bauta wa tsarin siyasa. Wasu suna jin cewa al’ummarsu ko ƙabilarsu ta fi na sauran mutane. Amma wannan ba gaskiya ba ne. (Ayukan Manzanni 10:34, 35) Wasu mutane suna juyawa ga ƙungiyoyin siyasa don su warware matsalolin mutane. Ta wurin yin haka, suna ƙin Mulkin Allah. Wanda shi ne kaɗai zai magance matsalolinmu.—Daniel 2:44.
6. Wata hanyar da Shaiɗan yake yaudarar mutane kuma ita ce ta wurin jarabtar su da sha’awar zunubi. Jehovah ya gaya mana mu guje wa ayyukan zunubi domin ya san cewa za su yi mana lahani. (Galatiyawa 6:7, 8) Wasu mutane za su so ka bi su cikin irin waɗannan ayyukan. Amma, ka tuna fa, Shaiɗan ne yake so ka yi waɗannan abubuwa.—1 Korinthiyawa 6:9, 10; 15:33. 7. Shaiɗan zai iya amfani da tsanantawa ko kuwa hamayya don ya sa ka bar Jehovah. Wasu da ka ke ƙauna za su iya fusata domin kana nazarin Littafi Mai-Tsarki. Wasu kuma za su yi maka ba’a. Amma wa ke da iko bisa ranka? Shaiɗan yana so ya tsoratar da kai domin ka daina koyo game da Jehovah. Kada ka bar Shaiɗan ya ci nasara! (Matta 10:34-39; 1 Bitrus 5:8, 9) Ta wurin hamayya da Iblis, za ka sa Jehovah ya yi farin ciki kuma za ka nuna cewa kana ɗaukaka ikon mallakarsa.—Misalai 27:11. |
||||
An Wallafa a Shekara ta 1996 |
|
Copyright © 2006 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania. All rights reserved. |
|