Dandalin Halal na Shaidun Jehobah

Gida Beliefs Future Medical Topics Contact Us Publications Languages
Menene Allah Yake Bukata a Garemu? Darasi na 6Talifa na bayaTalifi na gaba

Menene Mulkin Allah?

A wane wuri ne Mulkin Allah yake? (1)
Wanene kuma Sarkinta? (2)
Akwai waɗanda za su yi sarauta tare da Sarkin ne? Idan akwai, su nawa ne? (3)
Me ya nuna cewa muna rayuwa a cikin kwanaki na ƙarshe? (4)
Menene Mulkin Allah zai yi wa mutane a nan gaba? (5-7)

1. Lokacin da Yesu yake duniya, ya koya wa mabiyansa su yi addu’a don Mulkin Allah ya zo. Mulki gwamnati ce wadda sarki yake shugabanci. Mulkin Allah gwamnati ce ta musamman. An kafa ta a sama kuma za ta yi sarauta bisa wannan duniya. Za ta tsarkake sunan Allah. Za ta sa a yi nufin Allah a duniya kamar yadda ake yi a sama.—Matta 6:9, 10.

2. Allah ya yi alkawarin cewa Yesu ne zai zama Sarki a cikin Mulkinsa. (Luka 1:30-33) Lokacin da Yesu yake duniya, ya nuna cewa zai zama kamiltaccen Sarki, mai alheri, da kuma mai adalci. Lokacin da ya koma sama, ba a naɗa shi Sarkin Mulkin Allah nan da nan ba. (Ibraniyawa 10:12, 13) A shekara ta 1914, Jehovah ya ba Yesu ikon da Ya yi masa alkawari. Tun daga lokacin, Jehovah ya naɗa Yesu Sarki yana sarauta a sama.—Daniel 7:13, 14.

3. Jehovah ya zaɓe wasu amintattun mutane maza da mata daga duniya da za su je sama. Za su yi sarauta tare da Yesu, su yi alƙalanci, kuma su zama firistoci bisa ’yan Adam. (Luka 22:28-30; Ru’ya ta Yohanna 5:9, 10) Yesu ya kira abokan sarauta na Mulkinsa “ƙaramin garke.” Adadinsu 144,000 ne.—Luka 12:32; Ru’ya ta Yohanna 14:1-3.

4. Da Yesu ya zama Sarki, ya jefo Shaiɗan da miyagun mala’ikunsa daga sama zuwa duniya. Shi ya sa abubuwa suka lalace haka a duniya tun daga 1914. (Ru’ya ta Yohanna 12:9, 12) Yaƙi, yunwa, annoba, yaɗuwar mugunta—dukan waɗannan “alama” ce da ke nuna cewa Yesu yana sarauta kuma ke nuna cewa wannan zamani yana cikin kwanaki na ƙarshe.—Matta 24:3, 7, 8, 12; Luka 21:10, 11; 2 Timothawus 3:1-5.

5. Ba da daɗewa ba Yesu zai yi wa mutane shari’a, zai raba su kamar yadda makiyayi ke raba tumaki daga awaki. “Tumaki” sune waɗanda sun nuna kansu masu bin shi ne masu aminci. Za su sami rai na har abada a duniya. “Awaki” sune waɗanda suka ƙi Mulkin Allah. (Matta 25:31-34, 46) A nan gaba kaɗan, Yesu zai halaka dukan masu kama da awaki. (2 Tassalunikawa 1:6-9) Idan kana so ka zama ɗaya cikin “tumaki” na Yesu, dole ne ka saurara ga saƙon Mulkin kuma ka yi abin da ka koya.—Matta 24:14.

A ƙarƙashin sarautar Yesu, ba za a ƙara yin ƙiyayya ko kuwa wariya ba

6. A yau duniya ta rabu zuwa ƙasashe da yawa. Kowacce tana da gwamnatin kanta. Waɗannan al’ummai sau da yawa suna fāɗa da junansu. Amma Mulkin Allah zai sauya dukan gwamnatocin ’yan Adam. Shi kaɗai ne zai zama gwamnatin da za ta yi sarauta bisa dukan duniya. (Daniel 2:44) Sa’annan yaƙi, yin laifi, da kuma nuna ƙarfi ba za su ƙara kasancewa ba. Dukan mutane za su zauna tare cikin salama da haɗin kai.—Mikah 4:3, 4.

7. A lokacin Sarautar Yesu ta Shekara Dubu, amintattun mutane za su kamilta, dukan duniya kuwa za ta zama aljanna. A ƙarshen shekara dubun, Yesu zai kammala dukan abubuwan da Allah ya ce ya yi. Sai kuma ya mayar da Mulkin ga Ubansa. (1 Korinthiyawa 15:24) Me ya sa ba za ka gaya wa abokanka da waɗanda ka ke ƙauna game da abin da Mulkin Allah zai yi ba?

 

An Wallafa a Shekara ta 1996

GidaSamaTalifa na bayaTalifi na gaba

Copyright © 2006 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania. All rights reserved.