Dandalin Halal na Shaidun Jehobah

Gida Beliefs Future Medical Topics Contact Us Publications Languages
Menene Allah Yake Bukata a Garemu? Darasi na 7Talifa na bayaTalifi na gaba

Matsowa Kusa da Allah Cikin Addu’a

Me ya sa yin addu’a kullum yake da muhimmanci? (1)
Ga wanene ya kamata mu yi addu’a, kuma ta yaya? (2, 3)
Waɗanne batutuwa ne sun dace don addu’a? (4)
Da wane lokaci ne ya kamata ka yi addu’a? (5, 6)
Allah yana jin dukan addu’o’i ne? (7)

1. Addu’a yin magana ne da Allah cikin tawali’u. Ya kamata ka yi addu’a ga Allah kullum. Ta haka, za ka yi kusa da shi kamar da aboki na ƙwarai. Jehovah yana da girma da kuma iko, duk da haka yana jin addu’o’inmu! Kana addu’a ga Allah kullum kuwa?—Zabura 65:2; 1 Tassalunikawa 5:17.

2. Addu’a sashen bautanmu ne. Saboda haka, ya kamata mu yi addu’a ga Allah, Jehovah, shi kaɗai. Lokacin da Yesu yake duniya, yakan yi addu’a ko yaushe ga Ubansa ne, ba ga wani ba. Ya kamata mu ma mu yi haka . (Matta 4:10; 6:9) Amma dai, ya kamata mu yi dukan addu’o’inmu a cikin sunan Yesu. Wannan yana nuna cewa mun daraja matsayin Yesu kuma mun yi imani da hadayar fansar da ya yi.—Yohanna 14:6; 1 Yohanna 2:1, 2.

3. Yayin da muke addu’a ya kamata mu yi wa Allah magana daga zuciyarmu. Bai kamata mu haddace addu’armu ko kuwa mu karanta daga wani littafin addu’a ba. (Matta 6:7, 8) Muna iya yin addu’a a cikin ladabi, a kowane lokaci, kuma a kowane wuri. Allah yana jin addu’armu na zuci ma. (1 Samuila 1:12, 13) Yana da kyau mu nemi wurin da babu mutane don mu yi addu’a na kanmu.—Markus 1:35.

4. Waɗanne batutuwa ne za ka yi addu’a game da su? Dukan wani abin da zai iya shafan abokantakarka da shi. (Filibbiyawa 4:6, 7) Addu’ar misali ta nuna mana cewa ya kamata mu yi addu’a game da sunan Jehovah da ƙudurinsa. Za mu iya roƙo ya yi mana tanadin bukatunmu na jiki, ya gafarta mana zunubanmu, ya kuma taimaka mana kada mu fāɗa cikin jaraba. (Matta 6:9-13) Bai kamata addu’armu ta zama ta son kai ba. Ya kamata mu yi addu’a don abubuwan da sun yi daidai da nufin Allah.—1 Yohanna 5:14.

5. Za ka iya addu’a duk lokacin da zuciyarka ta motsa ka ka yi wa Allah godiya ko kuwa ka yaba masa. (1 Labarbaru 29:10-13) Ka yi addu’a yayin da ka ke da matsaloli da kuma lokacin da ka ke fuskantar gwaji na bangaskiyarka. (Zabura 55:22; 120:1) Ya dace ka yi addu’a kafin ka ci abinci. (Matta 14:19) Jehovah ya gayyace mu mu yi addu’a a “kowane loto.”—Afisawa 6:18.

6. Muna bukatar addu’a musamman ma idan mun yi babban zunubi. A waɗannan lokutta sai mu roƙi jinƙai da gafara daga wurin Jehovah. Idan mun bayyana masa zunubanmu kuma muka yi iyakacin ƙoƙarinmu don kada mu maimaita su, Allah “mai-hanzarin gafartawa” ne.—Zabura 86:5; Misalai 28:13.

7. Jehovah yana jin addu’ar masu adalci ne kawai. Domin Allah ya ji addu’o’inka, tilas ne ka yi ƙoƙarin rayuwa bisa ga dokokinsa. (Misalai 15:29; 28:9) Dole ka kasance da tawali’u, sa’anda ka ke yin addu’a. (Luka 18:9-14) Ya kamata ka yi aiki daidai da abin da ka yi addu’a a kai. Ta haka za ka nuna cewa kana da bangaskiya kuma kana da niyyar abin da ka faɗi da gaske. Ta haka ne kawai Jehovah zai amsa addu’o’inka.—Ibraniyawa 11:6.

 

An Wallafa a Shekara ta 1996

GidaSamaTalifa na bayaTalifi na gaba

Copyright © 2006 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania. All rights reserved.