| Menene Allah Yake Bukata a Garemu? | Darasi na 8 |
Rayuwar Iyali da Ke Faranta Wa Allah Rai |
|
| Menene matsayin maigida a cikin iyali? (1) | |
| Ta yaya maigida zai bi da matarsa? (2) | |
| Wace nawaya ce uba ke da shi? (3) | |
| Menene aikin uwargida a cikin iyali? (4) | |
| Menene Allah yake bukata a wurin iyaye da kuma yara? (5) | |
| Menene ra’ayin Littafi Mai-Tsarki game da rabuwa da kisan aure? (6, 7) | |
1. Littafi Mai-Tsarki ya ce namiji shi ne shugaban iyalinsa. (1 Korinthiyawa 11:3) Mace ɗaya tak namiji zai aura. Kuma ya kamata su yi aure daidai bisa doka.—1 Timothawus 3:2; Titus 3:1. 2. Ya kamata maigida ya ƙaunaci matarsa kamar yadda yake ƙaunar kansa. Ya kamata ya bi da ita kamar yadda Yesu ya bi da mabiyansa. (Afisawa 5:25, 28, 29) Bai kamata ya bugi matarsa ba ko ya wulaƙanta ta a kowace irin hanya. Maimakon haka, ya kamata ya ba ta girma da kuma daraja.—Kolossiyawa 3:19; 1 Bitrus 3:7.
3. Ya kamata uba ya yi aiki da ƙwazo domin ya kula da iyalinsa. Tilas ne ya yi tanadin abinci, sutura, da gida wa matarsa da yaransa. Dole ne kuma uba ya yi tanadi don bukatun ruhaniyar iyalinsa. (1 Timothawus 5:8) Shi zai yi ja-gora wajen taimaka ma iyalinsa su koya game da Allah da nufe-nufensa.—Kubawar Shari’a 6:4-9; Afisawa 6:4. 4. Ya kamata mace ta zama mataimakiya na ƙwarai ga mijinta. (Farawa 2:18) Ya kamata ta taimaki mijinta wajen koyarwa da kuma ɗabi’antar da yaransu. (Misalai 1:8) Jehovah ya bukaci mace ta kula da iyalinta cikin ƙauna. (Misalai 31:10, 15, 26, 27; Titus 2:4, 5) Ya kamata ta ba mijinta daraja sosai.—Afisawa 5:22, 23, 33. 5. Allah ya bukaci yara su yi biyayya ga iyayensu. (Afisawa 6:1-3) Yana bukatar iyaye su koyar da yaransu kuma su gyara su. Iyaye na bukatar zama tare da yaransu don su yi nazarin Littafi Mai-Tsarki da su, su biya masu bukatunsu na ruhaniya da kuma na jiye-jiyensu. (Kubawar Shari’a 11:18, 19; Misalai 22:6, 15) Bai kamata iyaye su hori yaransu cikin zalunci ko rashin tausayi ba.—Kolossiyawa 3:21.
6. Sa’anda mata da miji suka fuskanci matsaloli cikin aurensu, ya kamata su yi ƙoƙari su yi amfani da gargaɗin Littafi Mai-Tsarki. Littafi Mai-Tsarki ya aririce mu mu nuna ƙauna kuma muna gafartawa. (Kolossiyawa 3:12-14) Kalmar Allah ba ta goyi bayan rabuwa wajen warware ƙananan matsaloli ba. Amma mace za ta iya barin mijinta idan (1) ya kangare ya ƙi lura da iyalinsa, (2) idan yana dūkanta har lafiyarta da ranta na cikin haɗari, ko kuma (3) idan hamayyarsa ya kai ga hana ta bauta wa Jehovah.—1 Korinthiyawa 7:12, 13. 7. Tilas ne mata da miji su nuna aminci ga juna. Zina zunubi ne ga Allah da kuma ga matarka ko mijinki. (Ibraniyawa 13:4) Yin jima’i da ba a cikin aure ba shi ne dalili ɗaya tak na Nassi wanda za a iya kashe aure, da damar a sake yin wani aure. (Matta 19:6-9; Romawa 7:2, 3) Jehovah ba ya son mutane su kashe aure kuma su sake aure ba tare da wani dalili na Nassi ba.—Malachi 2:14-16. |
||||
An Wallafa a 1996 |
|
Copyright © 2008 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania. All rights reserved. |
|