| Menene Allah Yake Bukata a Garemu? | Darasi na 9 |
Tilas ne Bayin Allah Su Kasance da Tsabta |
|
| Me ya sa tilas ne mu kasance da tsabta a kowace hanya? (1) | |
| Me ake nufi da tsabta ta ruhaniya? (2) tsabta ta ɗabi’a? (3) tsabta ta hankali? (4) tsabta ta jiki? (5) | |
| Waɗanne ƙazaman maganganu ne ya kamata mu guje musu? (6) | |
1. Jehovah Allah ne mai tsabta da kuma tsarki. Yana so masu bauta masa su kasance da tsabta—a ruhaniya, ɗabi’a, hankali, da kuma a jiki. (1 Bitrus 1:16) Muna bukatar ƙoƙari sosai domin kasance da tsabta a idanun Allah. Muna zama a cikin duniya da ba ta da tsabta. Muna fama kuma da muradinmu na son yin laifi. Amma kada mu fid da rai.
2. Tsabta ta Ruhaniya: Idan muna so mu bauta wa Jehovah, ba za mu ci gaba da bin koyarwa ko al’adun addinin ƙarya ba. Dole ne mu fita daga cikin addinin ƙarya kuma mu ƙi goyon bayansa ta kowace hanya. (2 Korinthiyawa 6:14-18; Ru’ya ta Yohanna 18:4) Da zarar mun koyi gaskiya game da Allah, tilas ne mu mai da hankali kada mutane su yaudare mu da koyarwar ƙarya.—2 Yohanna 10, 11. 3. Tsabta ta Ɗabi’a: Jehovah yana son dukan masu bauta masa su nuna halin Kirista na gaskiya a kowane lokaci. (1 Bitrus 2:12) Yana ganin dukan abin da muke yi, ko a asirce. (Ibraniyawa 4:13) Ya kamata mu guje wa lalata ta jima’i da wasu ayyukan ƙazanta na wannan duniyar.—1 Korinthiyawa 6:9-11 4. Tsabta ta Hankali: Idan muka cika zukatanmu da tunani masu kyau, masu tsabta, halayenmu ma za su kasance da tsabta. (Filibbiyawa 4:8) Amma idan ya zama muna tunanin abubuwan da ba su da kyau, zai kai ga yin miyagun ayyuka. (Matta 15:18-20) Ya kamata mu guje ma fasalolin nishaɗi da za su ɓata tunaninmu. Za mu iya cika zukatanmu da tunani masu tsabta ta wurin nazarin Kalmar Allah. 5. Tsabta ta Jiki: Domin suna wakiltan Allah, ya kamata Kiristoci su kasance da tsabta a jiki da kuma tufafin su. Ya kamata mu wanke hannayenmu idan mun gama bayan gida, kuma mu wanke su kafin mu ci abinci ko kuma mu taɓa wani abinci. Idan ba ka da wurin bayan gida mai kyau, sai ka binne kashi sosai. (Kubawar Shari’a 23:12, 13) Tsabta tana ƙara lafiyar jiki. Gidan Kirista ya kamata ya kasance da tsabta sosai ciki da wajen. Ya kamata ya zama misali mai kyau ga maƙwabta. 6. Magana Mai Tsabta: Bayin Allah tilas ne suna faɗin gaskiya kullum. Maƙaryata ba za su shiga Mulkin Allah ba. (Afisawa 4:25; Ru’ya ta Yohanna 21:8) Kiristoci ba sa ƙazaman maganganu. Ba sa yi ko kuwa su saurari ƙazamin zolaya ko taɗi mara kyau. Domin furcinsu masu kyau ne, sun bambanta a wajen aiki ko a makaranta da kuma a unguwarsu.—Afisawa 4: 29, 31; 5:3.
|
An Wallafa a 1996 |
|
Copyright © 2008 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania. All rights reserved. |
|