Dandalin Shaidun Jehobah

Gida Beliefs Future Medical Topics Ka Tuntuɓe Mu Publications Languages
Menene Allah Yake Bukata a Garemu? Darasi na 11Talifa na bayaTalifi na gaba

Imani da Al’adu da Ke Ɓata Wa Allah Rai

Waɗanne imani da al’adu ne ba su da kyau? (1)
Ya kamata Kiristoci su gaskata cewa Allah Dunƙulin-Alloli-Uku ne? (2)
Me ya sa Kiristoci na gaskiya ba sa yin bikin Kirsimati, Ista, ko kuma bikin ranar haihuwa? (3, 4)
Matattu za su iya yi wa rayayyu lahani ne? (5)
Yesu ya mutu akan wani abin da aka giciyya ne? (6)
Yaya muhimmancin faranta wa Allah rai? (7)

Allah ba Dunƙulin-Alloli-Uku ba ne

1. Ba dukan imani da al’adu ba ne ba su da kyau. Amma Allah bai amince da su ba idan tushensu addinan ƙarya ne ko kuwa sun saɓa wa koyarwar Littafi Mai-Tsarki.—Matta 15:6.

2. Dunƙulin-Alloli-Uku: Jehovah Dunƙulin-Alloli-Uku ne—alloli uku cikin Allah ɗaya? A’a! Jehovah, Uba, shi ne “Allah makaɗaici mai-gaskiya.” (Yohanna 17:3; Markus 12:29) Yesu shi ne Ɗansa na fari, kuma yana biyayya ga Allah. (1 Korinthiyawa 11:3) Uban ya fi Ɗansa girma. (Yohanna 14:28) Ruhu mai-tsarki ba mutum ba ne; ikon da Allah yake aiki da shi ne.—Farawa 1:2; Ayukan Manzanni 2:18.

Kirsimati da Ista sun fito ne daga addinan ƙarya na dā
Babu wani dalilin bauta ko kuwa jin tsoron matattu

3. Kirsimati da Kuma Ista: Ba a ranar 25 ga Disamba ba ne aka haifi Yesu. Wataƙila an haife shi a ranar 1 ga Oktoba, a lokacin da makiyaya ke barin dabbobinsu a waje da daddare. (Luka 2:8-12) Yesu bai umurce Kiristoci su yi bikin haihuwarsa ba. Maimakon haka, ya umurce almajiransa su yi bikin tunawa da mutuwarsa. (Luka 22:19, 20) Kirsimati da al’adunsa sun fito ne daga addinan ƙarya na dā. Haka ma yake da al’adun Ista, irinsu amfani da ƙwai da zomaye. Kiristoci na farko ba su taɓa yin bikin Kirsimati ba ko kuma Ista, ba kuwa Kiristoci na gaskiya na yau ba.

4. Ranakun Haihuwa: Bikin ranar haihuwa guda biyu da aka ambata a cikin Littafi Mai-Tsarki ba masu bauta wa Jehovah ba ne suka yi. (Farawa 40:20-22; Markus 6:21, 22, 24-27) Kiristoci na farko ba su yi bikin ranakun haihuwa ba. An samo al’adar yin bikin ranar haihuwa daga addinan ƙarya ne na dā. Kiristoci na gaskiya suna ba da kyauta kuma holewa tare a wasu lokutta a cikin shekara.

5. Tsoron Matattu: Matattu ba za su iya yin kome ko kuwa su ji wani abu ba. Ba za mu iya mu taimake su ba, su kuma ba za su iya yi mana lahani ba. (Zabura 146:4; Mai-Wa’azi 9:5, 10) Kurwa tana mutuwa; ba ta rayuwa bayan mutuwa. (Ezekiel 18:4) Amma a wasu lokutta miyagun mala’iku, waɗanda ake kira aljanu, suna nuna kamar sune da gaske ruhun matattu. Dukan wani al’ada da take da wani alaƙa da tsoro ko kuwa bautar matattu ba ta da kyau.—Ishaya 8:19.

6. Gicciye: Yesu bai mutu akan wani abin da aka gicciya ba. Ya mutu akan miƙaƙƙen itace ne, ko gungume. Kalmar Hellenanci da aka juya “gicciye” a cikin Littafi Mai-Tsarki da yawa yana nufin katako ɗaya ne. Alamar gicciya ta fito ne daga addinan ƙarya na dā. Kiristoci na farko ba su yi amfani da gicciye ba ko kuwa su bauta masa. Saboda haka, kana jin daidai ne a yi amfani da gicciye wajen bauta?—Kubawar Shari’a 7:26; 1 Korinthiyawa 10:14.

7. Barin wasu imani da al’adu zai yi wuya ƙwarai. ’Yan’uwa da abokane za su yi ƙoƙari su rinjaye ka kada ka sauya imani da ka ke da shi. Amma faranta wa Allah rai ya fi faranta wa mutane rai muhimmanci.—Misalai 29:25; Matta 10:36, 37.

 

An Wallafa a 1996

GidaSamaTalifa na bayaTalifi na gaba

Copyright © 2010 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania. All rights reserved.