| Menene Allah Yake Bukata a Garemu? | Darasi na 13 |
Ta Yaya Za Ka Sami Addini na Gaskiya? |
|
| Dukan addinai ne suke faranta wa Allah rai, ko kuwa ɗaya ne dai kawai? (1) | |
| Me ya sa da akwai addinai da yawa da suke da’awar su Kiristoci ne? (2) | |
| Ta yaya za ka gane Kiristoci na gaskiya? (3-7) | |
1. Yesu ya kafa addinin Kirista na gaskiya guda ɗaya. Saboda haka tilas ne a yau a sami ƙungiya guda, ko kuwa rukuni, na masu bautar Jehovah Allah da gaske. (Yohanna 4:23, 24; Afisawa 4:4, 5) Littafi Mai-Tsarki ya koyar da cewa mutane kalilan ne suke a kan matsatsiyar hanyar zuwa rai.—Matta 7:13, 14. 2. Littafi Mai-Tsarki ya annabta cewa bayan mutuwar manzannin, koyarwar ƙarya da ayyukan da ba na Kirista ba za su shigo cikin ikklisiyar Kirista da sannu sannu. Mutane za su ja masu-bi su bi su maimakon su bi Kristi. (Matta 7:15, 21-23; Ayukan Manzanni 20:29, 30) Dalilin da ya sa ke nan muna ganin addinai da yawa da suke da’awar su Kiristoci ne. Ta yaya za mu gane Kiristoci na gaskiya? 3. Alama ta musamman na Kiristoci na gaskiya ita ce ƙauna ta gaskiya da suke da ita a tsakaninsu. (Yohanna 13:34, 35) Ba a koya masu tunanin cewa sun fi mutanen wasu ƙabilu ko masu launin fata dabam. Ba kuwa an koya masu ƙyaman mutanen wasu ƙasashe ba. (Ayukan Manzanni 10:34, 35) Saboda haka ba sa yin yaƙe-yaƙe. Kiristoci na gaskiya suna sha’ani da ’yan’uwa maza da mata.—1 Yohanna 4:20, 21.
4. Wata alamar addini na gaskiya ita ce daraja sosai da suke ba wa Littafi Mai-Tsarki. Sun yarda ita ce Kalmar Allah kuma sun gaskata abin da ta ce. (Yohanna 17:17; 2 Timothawus 3:16, 17) Sun ɗauki Kalmar Allah da muhimmanci fiye da ra’ayoyi ko kuwa al’adun ’yan Adam. (Matta 15:1-3, 7-9) Suna ƙoƙarin yin abin da Littafi Mai-Tsarki ya ce, a rayuwarsu na yau da kullum. Saboda haka, ba sa yin wa’azin abu dabam sa’annan kuma suna yin abu dabam.—Titus 1:15, 16. 5. Tilas ne kuma addini na gaskiya ya daraja sunan Allah. (Matta 6:9) Yesu ya sanar da sunan Allah, Jehovah, ga wasu. Tilas ne Kiristoci na gaskiya su yi hakan. (Yohanna 17:6, 26; Romawa 10:13, 14) Waɗanne mutane ne a yankinku suke gaya wa wasu game da sunan Allah? 6. Tilas ne Kiristoci na gaskiya su yi wa’azi game da Mulkin Allah. Yesu ya yi haka. Yana magana kullum game da Mulkin. (Luka 8:1) Ya umurce almajiransa su yi wa’azin wannan saƙon a dukan duniya. (Matta 24:14; 28:19, 20) Kiristoci na gaskiya sun gaskata cewa Mulkin Allah ne kawai zai kawo salama da kwanciyar rai ga wannan duniya.—Zabura 146:3-5. 7. Dole ne almajiran Yesu su kasance su ba na wannan muguwar duniya ba. (Yohanna 17:16) Ba sa saka hannu cikin harƙoƙin siyasa da kuma hargitsi na zaman jama’a. Suna guje ma halaye, ayyuka, da kuma abubuwan lahani da ake yi a ko’ina cikin wannan duniyar. (Yaƙub 1:27; 4:4) Za ka iya gano rukunin addini a yankinku da yake da alamun nan na Kiristanci na gaskiya? |
||
An Wallafa a Shekara ta 1996 |
|
Copyright © 2006 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania. All rights reserved. |
|