| Menene Allah Yake Bukata a Garemu? | Darasi na 16 |
Shawararka ta Bauta Wa Allah |
|
| Menene ya zama dole ka yi don ka zama abokin Allah? (1, 2) | |
| Ta yaya za ka keɓe kanka ga Allah? (1) | |
| Yaushe ya kamata ka yi baftisma? (2) | |
| Ta yaya za ka sami ƙarfi don ka ci gaba da bangaskiyarka ga Allah? (3) | |
1. Don ka zama abokin Allah, dole ne ka sami isashen sani na Littafi Mai-Tsarki (1 Timothawus 2:3, 4), ka ba da gaskiya ga abubuwan da ka koya (Ibraniyawa 11:6), ka tuba daga zunubanka (Ayukan Manzanni 17:30, 31), ka kuma juya daga irin rayuwarka ta dā. (Ayukan Manzanni 3:19) Sai ƙaunarka ga Allah ta motsa ka ka keɓe kanka gareshi. Wannan yana nufin cewa a cikin addu’arka za ka gaya masa cewa yanzu ka ba da kanka gareshi don ka yi nufinsa.—Matta 16:24; 22:37. 2. Bayan ka keɓe kanka ga Allah, sai ka yi baftisma. (Matta 28:19, 20) Baftisma tana sanar da kowa cewa ka keɓe kanka ga Jehovah. Saboda haka, baftisma don waɗanda suka yi girma ne kawai, waɗanda za su iya zaɓa da kansu su bauta wa Allah. Sa’anda ake yi ma mutum baftisma, za a nutsar da shi cikin ruwa na ɗan lokaci.*—Markus 1:9, 10; Ayukan Manzanni 8:36. 3. Bayan ka keɓe kanka, Jehovah zai bukaci ka yi rayuwarka daidai da alkawarin da ka yi. (Zabura 50:14; Mai-Wa’azi 5:4, 5) Iblis zai yi ƙoƙarin ya hana ka bauta wa Jehovah. (1 Bitrus 5:8) Amma ka matso kusa da Allah cikin addu’a. (Filibbiyawa 4:6, 7) Ka yi nazarin Kalmarsa kowace rana. (Zabura 1:1-3) Ka manne wa ikklisiya. (Ibraniyawa 13:17) Ta wurin yin dukan waɗannan, za ka samu ƙarfin da za ka ci gaba da bangaskiyarka ga Allah. Da haka, za ka iya yin abubuwan da Allah yake bukata a gareka har abadan abadin! Za ka so ƙarin bayani ko kuma nazarin Littafi Mai Tsarki kyauta a gida? Ka rubuta zuwa ga Shaidun Jehovah da adireshi da ya dace. Adireshi
|
||
An Wallafa a Shekara ta 1996 |
|
Copyright © 2006 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania. All rights reserved. |
|